Jin Kim 공개
[search 0]

Download the App!

show episodes
 
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
 
Loading …
show series
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne kan yadda wata matashiya a jihar Kanon Najeriya ta kirkiri manhajar da ke kwarmata rahotanni game da masu fyade. Ana amfani da manhajar ne mai suna Helpio a wayoyin hannu. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken bayani kan dalilin da ya sa matashiyar mai shekaru 20 ta samar da wannan …
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako tare da Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali ne kan barazanar da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta yi na sake komawa yajin aiki. Malaman sun yi korafin cewa gwamnati ta ki cika alkawurran da ta dauka musu, sannan tana muzguna wa mambobinta.저자 RFI Hausa
 
Albarkacin bikin ranar mata ta duniya, shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' tare da Bashir Ibrahim idris ya yi dubi ne da ilimin 'yaya mata da kuma matsalolin da ya ke fuskanta a Najeriya. A wannan shirin, ya leka jihar Kaduna ne, don jin irin tsare-tsaren da hukumomi ke yi don inganta ilimin 'yaya mata, musamman ma a yanayi na rashin tsaro wanda yake sany…
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris ya cigaba da tattaunawa kan matashin nan dan Jihar Kano Sa'id Ahmad ya kera jirgin sama marar matuki. Cikin shirin na wannan lokaci za a ji tattaunawa da mutanen da suka shaida gagarumin aikin matashin저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa a wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya cigaba da tattaunawa kan irin kokarin da kamfanonin harhada magunguna ke yi na samar da maganin cutar ta coronavirus wadda ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa a wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tabo irin kokarin da kamfanonin harhada magunguna ke yi na samar da maganin cutar ta coronavirus wadda ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa na makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora kan na makon jiya da ya mayar da hankali kacokan game da nasarar da wani matashi na Dan Najeriya ya yi ta kera na'urar da za ta taimakawa. Ayi Saurare Lafiya.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora kan na makon jiya, da ya tabo kalubalen da ilimi ke fuskanta a kasashe masu tasowa musamman masu fuskantar rikici ciki har da Najeriya dai dai lokacin da Duniya ke bikin ranar malamai ta Duniya.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa a karon tare da Bashir Ibrahim Ibrahim Idris ya yi duba kan bikin ranar Malamai ta Duniya da ke gudana kowacce ranar 5 ga watan Oktoba, dai dai lokacin da ilimin dungurugum ke fuskantar barazana musamman a yankunan da ke fama da rikici.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, inda yake nazari kan matakin da gwamnatin jihar Jigawa da ke Najeriya ta dauka na janye tallafin da kananan hukumomin jihar ke bayarwa domin taimaka wa 'ya'yan talakawa samun ilimi a jami'ar jihar.저자 RFI Hausa
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan matakin da gwamnatin jihar Jigawa da ke Najeriya ta dauka na janye tallafin da kananan hukumomin jihar ke bayarwa domin taimaka wa 'ya'yan talakawa samun ilimi a jami'ar jihar.저자 RFI Hausa
 
Loading …

빠른 참조 가이드

Google login Twitter login Classic login